Shacin Fannonin Akadamiya

Shacin Fannonin Akadamiya
Wikimedia outline article (en) Fassara
Hadin n hotuna masu wakiltar fannonin akadamiya daban-daban

  Nau'in akadamiya ko fannin karatu wani reshe ne na ilimi da ake koyarwa da bincikawa a matsayin wani bangare na ilimi mai zurfi. Yawanci tsangayoyin Jami'a da ilimantattun al'umomin da suke ciki da mujallun akadamiya da suke wallafa bincikensu ke kayyade fannin karatun Masana.

Fannoni suna bambanta tsakanin kafaffun da ake samu a kusan dukkanin jami'o'i kuma suna da tsararrun rostoci na mujallu da tarurruka, da masu tasowa wadanda anda wasu jami'o'i da wallafe-wallafe kadan ne kawai ke gudanar da su. Wani fanni na iya samun rassa, kuma ana kiran wadannan sau da yawa kananan-fannuka.

An bayar da wannan shacin a matsayin bayyani na da kuma jagorar maudu'i ga fannukan akadamik. A kowane hali shigarwa a matakin mafi girma na matsayi (misali, Ilimin-Bil'adama) rukuni ne na faffdaddun fannuka makusanta; shigarwa a matsayi mafi girma na gaba (misali, Musika) fanni ne da ke da dan yancin kai da kuma kasancewa ainihin huwiyar asali da masanansa suke ji; da kuma Kananan matakai na hairakin wadanda mafi akasari ba su da wani tasiri a cikin tsarin gudanarwar jami'a.


© MMXXIII Rich X Search. We shall prevail. All rights reserved. Rich X Search